30 Mayu 2021 - 13:27
​Syria: Assad Yana Ci Gaba Da Samun Sakonnin Taya Murna Daga Shugabannin Kasashen Duniya

Shugaba Bashar Assad na Syria yana ci gaba da samun sakonnin taya murnar lashe zaben shugaban kasar da ya yi daga shugabannin kasashen duniya daban-daban.

ABNA24 : Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, tun bayan da hukumar zabe ta kasar Syria ta sanar a jiya kan cewa shugaba Assad ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a kasar, shugabannin kasashe daban-daban da suke da kyakkayawar alaka da Syria suke ci gaba da aikewa dasakonnin taya murna gare shi.

Shugaba Putin na Rasha ne ya fara aike masa da sakon taya murna, bayansa kuma shugabannin kasashen China, Iran, Venezuela, Cuba, Volivia, Abkhazia, Belarussia, Lebanon da sauransu.

A cikin sakon da ya aikewa shugaba Assad a yau Asabar, shugaban kasar Koriya ta arewa Kim Jong Un ya bayyana cewa, nasarar da shugaba Assad ya samu nasara ce ba kawai ta lashe zabe ba, nasara ce a kan makircin dukkanin kasashen duniya masu girman kai da suka kwashe shekaru suna shirya wa Syria makirci da nufin rusa ta, saboda taki ta zama ‘yar amshin shata kamar yadda wasu suka zama.

Shi ma a nasa sakon zuwa Assad, shugaban Falastinawa Mamhud Abbas ya bayyana cewa, nasarar Bashar Assad nasara ce ga al’ummar falastinu, samakon sadaukarwar da shugaba Assad ya yi domin al’ummar Falastinu.

Masu bin diddigin lamurra na ganin cewa, yadda aka gudanar da zaben kasar Syria lami lafiya ba tare da wani tashin hankali ko hare-haren ‘yan ta’adda ba, wannan wata manuniya a kan cewa an kawo karshen ‘yan ta’adda masu da’awar jihadi a kasar, wadanad suke samun goyon bayan kasashen yammacin turai da wasu sarakunan larabawa.

342/